If there are images in this attachment, they will not be displayed. Download the original attachment
A cikin shekarar da ya wuce ne yan uwa da abokan arziki suka yi dafifi
zuwa garin Katsina auren Ali da Mabruka.Biki son kowa kin wanda ya rasa.
Amarya da ango sun dace suna ta soyyayarsu irin ta kuruciya.Ba a shekara
ba sai ga Mabruka ta dawo gida da kayanta karkaf da jiki duk raunuka.Binciken
iyaye ya nuna cewa ango da amarya suna son junansu ama da yake suna
zaune a gidan gado ne wasu kanen Ali su ka adabi gidan da sace sace
da kuma shaye shaye.Ko takalmi Mabruka ta bari a waje ya tafi kenan
gashi idan suka yi shaye shayen idanuwan su ba sa kallon kowa da gashi
a ka har ya kai suka dake ta.Wannan labari ya daga wa jamaa hankali
ba dan komai ba sai dan kanen Ali’n nan duk mata ne kuma ba wace shekarunta
ya wuce 24.Guda biyu yan makaranta ne daya kuma bazzawara.A kamaninsu
da kyar a gane.Mahaifiyarsu ta yi iyaka kokarinta ta gane me ke sa su
hauka wani lokaci wani lokaci kuma dacin rai ta kasa ganewa,bata ganin
su da giya, kwayoyi ko taba.Anyi musu ruqiya dan Kore jinnu shiru.
Wannan matsala ya zama ruwan dare yanzu a al ummar mu.Bahaushe na
cewa rashin sani shi ne cuta,abun da ba a gane shi ba ai ba ranar maganin
shi.Ama a yanzu yawan aukuwar birkicewan jamaa ya sa an fara gane matsalolin.A
da idan aka ga mutum na wasu halaye marasa kan gado sai a ce yana shan
giya, wiwi ko hodar iblis;gaba gaba kwayoyi suka zo suka yi karfi irin
su LSD,ecstasy,meth,mai reverse,duniya komai level da dai sauransu.
Yanzu babu alamari mai daga hankali Kaman cewa maganin da aka fi amfani
da shi wurin fita daga hayaci da maye magani ne da ake samu a kusan
kowane gida.magani ne da ko dan shekara goma ya shiga chemist za a bashi
tunda magani ne da a da baya bukatar takardan likita.Nigeria kuma kasa
ce da babu doka saboda haka mutum zai iya samun ko guda nawa ya ke so
a kusan kowane lokaci. Masu shan wayannan magani ana kiransu yan parkalin,yan
tutolin,yan benylin ,yan codeine ko kuma slow.
Mura dai ciwo ne da kusan kowa na yi a kalla sau hudu a shekara,saboda
haka sayar da maganin mura dinnan ya zama dole .Matsalar shi ne yanda
wasu suke bata shi mayar da shi abun sa maye. Yawancin maganin mura
idan kuka duba za ku ga cewa suna maganin murar,tari,zazzabin murar
ta hanyar sa mutum barci ko kuma ya rage wa mutum zafin nama. Jikin
mutum sai ya dan yi sanyi wasu kuma su yi ta barci idan sun sha.
A cikin hirar da na yi da Mal Idris a Unguwar rimin Kaduna ya bayyana
mana cewa yawancin masu shan maganin nan dan suyi barci ne ko su manta
matsalolin rayuwa.wasu kuma ji suke idan sun sha tamkar basu da wata
matsala.Wasu kuma idan suka sha maganin murar ya kashe musu jiki sai
su hada da wasu kwayoyi kuma daban da ke sa su jin waras irin su a rungumi
zaki.Refnol,exol,roche,bashi,tramol wayanda duk kayan sa maye ne yawancinsu
magungunan asibiti ne ama idan aka sha su ba a dai dai ba akwai matsala.Mal
Idris ya dade yana wa matasa fada akan illolin shan kwayoyi kuma ya
kan binciki sababbin salo da suke fitowa da su kullum.
Ba matasa kade ke shan wayannan magungunan ba dan su samu su
yi slow dinnan a yanda suke fada.Masifa ce da ba babba ba yaro, ma
mace ba namiji ba mai kudi ba talaka.
A cikin hirar da muka yi da wasu yan sanda WCPL Evelyn da abokin aikinta
sun bayyana mana cewa a chemist ba a sayar da magungunan nan haka sidan
ama ana sayar da su ta bayan fage.Na tambayesu irin magungunan da ake
yayin sha a gari yanzu sun yi mana bayanin cewa akwai mogadon ,refnol,exol,kofsil.Na
kara tambayar su yanda suke gane masu shaye shayen nan? Sun yi min bayani
da cewa ya danganta,wasu idan sun har hada magungunan sai barci,wasu
kuma su yi slow din, wasu kuma su kara karfi da kuzari wasu kuma idan
hadin ya kwacibe har yi suke Kaman masu farfadiya.Idan su ka samu irin
yan shaye shayen nan wasu ana kaisu police station idan kuma sun rika
ana kai su har kotu.Idan kotu ta yanke hukunci kuma takan daure mutum
tun balanta idan shaye shayen ya hadu da wani babban cin mutunci Kaman
cin zarafin wani,sata,hatsari, ji ma wani rauni,zagi,fada,ko ta da husuma.
Matsalar nan ta shaye shayen maganin da ke iya sa maye ba a kasar
hausa ta fara ba;masifa ce da akwai ta a kowace kasar duniya,tun balanta
a inda ake da akida ta mutunci sai a fake da shan wayannan magunguna
a maimakon giya da su cocaine da wiwi.Wayannan magunguna basu da wani
wari ko alaman an sha su sai dai dabiar wanda ya sha idan ya chanza
an ga ba yanda yake kullum ba ko kuma idan bai sha ba yayi ta kunci
ko fada da mutane.
Menene sakamakon shaye shayen maganin asibiti ba da dalili ba ko kuma
a kan wata manufa daban da samun warkewar ciwo?In ji Dr Ahmad Inuwa
na Garko clinic Danladi Nasidi housing estate Kano ya ce, ‘’Hankali
shi ne mutum .Idan mutum ba ya cikin hayacinsa ba abun da ba zai iya
yi ba.A kiwon lafiya magungunan nan da aka mayar na maye ko zuga mutane
suna da amfani sosai idan aka bi kaidar su; wasu na ciwon jiki ne wasu
kuma maganin mura wasu na sa barci wasu kuma na hauka ne ma. Idan mutum
yana amfani da su ba a bisa kaida ba sai ya zamanto jikin sa ya saba
har ya zamanto kullum kwakwalwar sa na bukatar sai ya sha.Magungunan
sun kasu kashi daban daban da akwai wayanda ake kira opiods irin su
methadone ana amfani da su ne dan maganin zafin ciwo Kaman mumunar rauni
ko bayan an yi wa mutum theatre.Idan aka zarce da sha ya wuce kaida
sai ya zamanto wa mutum farilla ya sha kuma zai yi koma menene dan ya
samu.Shan su dayawa kuma yana iya kawo yankewar num fashi ko kuma mutuwa
farad daya.”Likita ya yi mana bayani.
“Depressants kuma irin su diazepam,lorazepam da dai sauransu ana
bada su a asibiti ne domin kwantar wa mutum da hankali da samo mishi
sauki idan yana fama da fargaba ko kasa barci.Idan ya zama jiki kuma
sai mutum ya sha kullum ya na sa yawan barci,rashin kuzari rudewa ,tabin
hankali .Hadarin neman a daina sha ba da zuwa asibiti ba idan ya zama
jiki kuma shi ne zai iya kawo lahani saboda haka idan an ga ne dan kwaya
irin wannan magungunar ya ke sha a kai shi asibiti dan likita ya kulla
da yanda za a raba mai sha da wannan halin.”
Abu Sufyan tsohon dan kwaya ne mai kokarin ya daina saboda haka sai
naga ya kamata muji daga bakin sa me ke sa su shan maganin asibiti ba
da dalili ko izinin likita ba me suke ji idan su kayi shaye shayen?
ya wahalar daina sha da kuma farashin magungunan.
Ya bayyana mana cewa,“Yawancin mutane wani damuwa ko baccin rai
ke sa su su fara shaye shaye ko son samun wani Karin karfin jiki ko
karfin guiwa idan za su je wani wuri ko za su yi wani muhimmin abu ama
daga baya sai ya zamanto wa mutum jiki kuma ko nawa ne zai sa kudi ya
saya.Magungunan basu da tsada irin su lara,d5,diyaga,assage,fashion
duk daga naira 10 ne zuwa naira 30.Masu tsada irin su babban tramol
ne wanda ake sayar wa N200.magungunan mura kuma daga N150 ne ama original
daga N500 su ke.Gaskiya daina sha na da wuya domin matsalolin rayuwa
dayawa.kwayan diyaga guda daya da ake sayarwa N20 sai ya warware maka
duk wani damuwa da kake ciki.”Abu Sufyan.
Samari,yan mata da matan aure sun fi zake wa a wurin shan maganin
mura dan maye ,idan aka je wasu wuraren shakatawa wayanda yan mata da
samari ke zagayawa a dare guda sai a samu kwalban magani 100 a lokaci
guda.Budurwa daya ana iya samun kwalba 5 a jakanta.Wasu matan auren
kuma haka su ma suke tara kwalaben magungunan nan su yi ta sha sun mayar
da shi Kaman sobo.
Ina iyayen da ke ba yaransu kudi su je su sha shisha?to su ma su kula
domin shisha grade B magunguna ake sawa aciki kar yaran ku su tashi
daga grade A wanda kanshi suke zuka ko kuma su koma grade C wanda wiwi
ake sawa a ciki.
Wasu na fakewa da cewa shan magani ba haramun bane tunda ba giya bane.wannan
babban kuskure ne domin babbu addinin da zai yarda da mutum ya sa kansa
a hali na maye ko bata rayuwarsa.Magani kyan sa mutum ya sha iyyaka
kai’dan da masana su ka bada ba wai ka ji labarin wani kwaya na sa
barci ka kama sha ba kulla ba.
Maganin wannan illa kuma na farko shi ne fadakarwa,idan jamaa duk
aka farga za a iya sa ido domin samun maganin wanan musiba da buwayi
al-umma.a rika kulawa da yara da irin mutanen da suke muammala da.Idan
an ga chanjin yanayi ko da mutum ya karyata shan kwaya haka siddan a
je asibiti a bincika.