Showing posts with label Cin zarafi. Show all posts
Showing posts with label Cin zarafi. Show all posts

Wednesday, 23 May 2012

KE WACCE CE. (WHO ARE YOU?)


“Ke wacce ce?Ke din banza! kina mace ki ce za ki gaya min abun da zan yi, ko ya kamata in yi? Kin fara hauka ne?Uban ki ma bai isa ya gaya min abun da zan yi ba balantana ke,sha sha sha, sakarya kawai, daba.”

Wannan kadan na dauko daga cikin shariar wani aure da aka yi a gaba na.Mata ce ta ba wa mijin ta shawara akan yan da zai rika tafiyar da harkokin sa na kasuwan ci tunda kowa ya san yau da wuya komai yayi tsamari a kasar.Da mijin ya tashi zagi ,mahaifinta ma sai da aka zage shi bai ji ba bai gani ba. Wannan shi ne Nasara ke kira abusive relationship wato dangantaka da ake yi wa cin mutunci ko cin zarafi.Me ke kawo cin zarafi tsakanin maaurata?Ina neman Karin bayani da haske dan mu samu mu fahimci wannan mumunar dabiar ta wasu maza da mata a gidajen su domin kokarin magance shi.