“Ke wacce ce?Ke din banza! kina mace ki ce za ki gaya min
abun da zan yi, ko ya kamata in yi? Kin fara hauka ne?Uban ki ma bai isa ya gaya
min abun da zan yi ba balantana ke,sha sha sha, sakarya kawai, daba.”
Wannan kadan na dauko daga cikin shariar wani aure da aka yi
a gaba na.Mata ce ta ba wa mijin ta shawara akan yan da zai rika tafiyar da
harkokin sa na kasuwan ci tunda kowa ya san yau da wuya komai yayi tsamari a
kasar.Da mijin ya tashi zagi ,mahaifinta ma sai da aka zage shi bai ji ba bai
gani ba. Wannan shi ne Nasara ke kira abusive relationship wato dangantaka da
ake yi wa cin mutunci ko cin zarafi.Me ke kawo cin zarafi tsakanin maaurata?Ina
neman Karin bayani da haske dan mu samu mu fahimci wannan mumunar dabiar ta
wasu maza da mata a gidajen su domin kokarin magance shi.