Friday 13 July 2012

AMFANI DA NAURAR BINCIKE NA GOOGLE


AMFANI DA NAURAR BINCIKE NA GOOGLE
Duk wani mai amfani da yanar gizo ya kamata a ce ya fahimci naurar bincike na Google domin shine uban dakin duk wani naurar bincike da ke kan yanar gizo wato intanet. Akwai naurorin bincike kala daban daban irin su Yahoo, bing, ask da dai sauran su, ama idan akace uban dakinsu kun san cewa ya sha gaban su ya yi masu shal inji kanawa. Kusan duka wani bayani a kan abubuwa wato ma’ana kama da sauran labaru a kan abubuwa za a same su a kan yanar gizo misali shine kaman idan kana son tarihin wani ko wata a nan bari in yi misali da Sarkin Kano Mai Martaba Ado Bayero.
Idan ka/ki na da waya mai aiki da intanet ko kuma komputa wanda an saka mashi layi mai intanet  kuma an biya kudin browsing sai a bude shafin yanar gizo a rubuta www.google.com a dana inda aka sa a dana a gefen dama wani lokaci ana rubutawa da harshen turanci cewa a dana a wasu wuraren kuma alama ce kawai idan shafin ya fito za ku gan an rubuta Google a saman wani dogon gida idan za ka rubuta abun da ka/ki ke so ku bincika.
 A saman wannan sunan Google din akwai inda aka yi wasu rubutu inda ake tambaya a kan bincike da za ka yi hotone? Labari ne? ko bincike a kan yanar gizo?
A kasa kuma idan kai mazaunin Najeriya ne za ka gan an rubuta harshen Hausa, Yoruba da Igbo, wato mutum ya zabi wanda ya ke so, zai kuma fi fahimta ba dole sai da harshen turanci ba, tun da munce bincike mu ke so muyi a kan Sarkin Kano Ado Bayero, sai kawai mu rubuta Sarkin kano ko mu rubuta Ado Bayero sai mu kuma dana inda aka rubuta search wato bincike kenan, cikin gajeren lokaci za ku gani bayani dubunai akan Sarkin Kano, sai dai mutum ya zabi wanda zai fi mai amfani ya karanta za a iya bude shafin yanar gizon da ya fi kusa da abun da a ke so a samu wasu lokutan har a kwafa a komfuta ko waya. Wasu  binciken  kuma sai dai a karanta a barshi.   
A cikin misali na Sarkin Kano za a ga hotuna,tarihi,labaru daga jaridu daban daban,film na video da aka dauke shi a wurare daban daban da dai sauransu.
Wani misali kuma shi ne kamar mutum na son samun bayani a kan wani ciwo ko magani ,mudin ciwon ko maganin sananne ne idan a ka rubuta sunan bayanai za su fito dalla dalla.
Uwargida kina son ki san amfanin wani abinci ko yadda za ki girka shi?
Wannan ma abu mai sauki ne,idan ki ka fara samo girki iri iri daga kasashen duniya da biki taba ma sanin sunayensu ba,maigida sai ya baki hakuri ya ce ya gode canji kulum a dawo miyar kukan nan dai ta gargajiya dan ya manta kamar ta. Bincike ki ke so akan kwalliya?Kula da gida,Tarbiyyar yara,Jan hankalin maigida da gyara zamantakewar ku duk ki bincika za ki samu na kasashe daban daban sai ki zabi wanda ya dace da akidar ku.
Yan makaranta kuna neman Karin bayani akan abubuwan da aka koya muku a aji ko an ba ku aiki ku yi a gida? To ku doshi Google duk wani karatu za ku tar da shi a bayane daga na yan shekaru biyu har kurewar boko.
Bincike kan ilimin addini  da na kimiya  ma duk da akwai idan aka bincika.
Akwai bayanai da mutum zai iya samu ta fanin sana’a kamar a ina zai samu masu sayan Ridin da ya ke nomawa,ta yaya zai gyara noman na shi?. A wace kasa a ka fi samun kayan aikin gona da yake nema.A wane shago ne ake samun shadda a sari wanda mutum zai iya oda ba sai ya je da kansa ba. Abubuwan dai  ba a cewa komai.
Ama fa duk abun da aka ce barka da shi kila a ce Allah ya wadaran sa domin ba duk abun da aka saka a kan yanar gizo ne ya ke zama gaskiya ba wasu da akwai karya da zamba saboda haka sai mutum ya kula ya yi amfani da hankalinsa.
Wajen binciken yara kuwa sai a yi kokarin jan kunnen su domin da akwai miyagun abubuwa na batsa da batanci da bai kamata su rika bincikawa ba suna budewa.Wannan aikin iyayene shi yasa yake da muhimmanci mu kanmu mu gane kan komfuta da irin su Google din mu dakanmu.

No comments:

Post a Comment