Monday 25 February 2013

SHAYE SHAYEN MAGUNGUNA MASU FITAR DA MUTANE DA GA HAYACINSU

If there are images in this attachment, they will not be displayed.  Download the original attachment
 
A cikin shekarar da ya wuce ne yan uwa da abokan arziki suka yi dafifi zuwa garin Katsina auren Ali da Mabruka.Biki son kowa kin wanda ya rasa. Amarya da ango sun dace suna ta soyyayarsu irin ta kuruciya.Ba a shekara ba sai ga Mabruka ta dawo gida da kayanta karkaf da jiki duk raunuka.Binciken iyaye ya nuna cewa ango da amarya suna son junansu ama da yake suna zaune a gidan gado ne wasu kanen Ali su ka adabi gidan da sace sace da kuma shaye shaye.Ko takalmi Mabruka ta bari a waje ya tafi kenan gashi idan suka yi shaye shayen idanuwan su ba sa kallon kowa da gashi a ka har ya kai suka dake ta.Wannan labari  ya daga wa jamaa hankali ba dan komai ba sai dan kanen Ali’n nan duk mata ne kuma ba wace shekarunta ya wuce 24.Guda biyu yan makaranta ne daya kuma bazzawara.A kamaninsu da kyar a gane.Mahaifiyarsu ta yi iyaka kokarinta ta gane me ke sa su hauka wani lokaci wani lokaci kuma dacin rai ta kasa ganewa,bata ganin su da giya, kwayoyi ko taba.Anyi musu ruqiya dan Kore jinnu shiru.
Wannan matsala ya zama ruwan dare yanzu a al ummar mu.Bahaushe na cewa rashin sani shi ne cuta,abun da ba a gane shi ba ai ba ranar maganin shi.Ama a yanzu yawan aukuwar birkicewan jamaa ya sa an fara gane matsalolin.A da idan aka ga mutum na wasu halaye marasa kan gado sai a ce yana shan giya, wiwi ko hodar iblis;gaba gaba kwayoyi suka zo suka yi karfi irin su LSD,ecstasy,meth,mai reverse,duniya komai level da dai sauransu.
Yanzu babu alamari mai daga hankali Kaman cewa maganin da aka fi amfani da shi wurin fita daga hayaci da maye magani ne da ake samu a kusan kowane gida.magani ne da ko dan shekara goma ya shiga chemist za a bashi tunda magani ne da a da baya bukatar takardan likita.Nigeria kuma kasa ce da babu doka saboda haka mutum zai iya samun ko guda nawa ya ke so a kusan kowane lokaci. Masu shan wayannan magani ana kiransu yan parkalin,yan tutolin,yan benylin ,yan codeine ko kuma slow.
Mura dai ciwo ne da kusan kowa na yi a kalla sau hudu a shekara,saboda haka sayar da maganin mura dinnan ya zama dole .Matsalar shi ne yanda wasu suke bata shi mayar da shi abun sa maye. Yawancin maganin mura idan kuka duba za ku ga cewa suna maganin murar,tari,zazzabin murar ta hanyar sa mutum barci ko kuma ya rage wa mutum zafin nama. Jikin mutum sai ya dan yi sanyi wasu kuma su yi ta barci idan sun sha.
A cikin hirar da na yi da Mal Idris a Unguwar rimin Kaduna ya bayyana mana cewa yawancin masu shan maganin nan dan suyi barci ne ko su manta matsalolin rayuwa.wasu kuma ji suke idan sun sha tamkar basu da wata matsala.Wasu kuma idan suka sha maganin murar ya kashe musu jiki sai su hada da wasu kwayoyi kuma daban da ke sa su jin waras irin su a rungumi zaki.Refnol,exol,roche,bashi,tramol wayanda duk kayan sa maye ne yawancinsu magungunan asibiti ne ama idan aka sha su ba a dai dai ba akwai matsala.Mal Idris ya dade yana wa matasa fada akan illolin shan kwayoyi kuma ya kan binciki sababbin salo da suke fitowa da su kullum.
Ba matasa kade ke shan wayannan magungunan ba  dan su samu su yi slow dinnan a yanda suke fada.Masifa ce da ba babba ba yaro, ma mace ba namiji ba mai kudi ba talaka.
A cikin hirar da muka yi da wasu yan sanda WCPL Evelyn da abokin aikinta sun bayyana mana cewa a chemist ba a sayar da magungunan nan haka sidan ama ana sayar da su ta bayan fage.Na tambayesu irin magungunan da ake yayin sha a gari yanzu sun yi mana bayanin cewa akwai mogadon ,refnol,exol,kofsil.Na kara tambayar su yanda suke gane masu shaye shayen nan? Sun yi min bayani da cewa ya danganta,wasu idan sun har hada magungunan sai barci,wasu kuma su yi slow din, wasu kuma su kara karfi da kuzari wasu kuma idan hadin ya kwacibe har yi suke Kaman masu farfadiya.Idan su ka samu irin yan shaye shayen nan wasu ana kaisu police station idan kuma sun rika ana kai su har kotu.Idan kotu ta yanke hukunci kuma takan daure mutum tun balanta idan shaye shayen ya hadu da wani babban cin mutunci Kaman cin zarafin wani,sata,hatsari, ji ma wani rauni,zagi,fada,ko ta da husuma.
Matsalar nan ta shaye shayen maganin da ke iya sa maye ba a kasar hausa ta fara ba;masifa ce da akwai ta a kowace kasar duniya,tun balanta a inda ake da akida ta mutunci sai a fake da shan wayannan magunguna a maimakon giya da su cocaine da wiwi.Wayannan magunguna basu da wani wari ko alaman an sha su sai dai dabiar wanda ya sha idan ya chanza an ga ba yanda yake kullum ba ko kuma idan bai sha ba yayi ta kunci ko fada da mutane.
Menene sakamakon shaye shayen maganin asibiti ba da dalili ba ko kuma a kan wata manufa daban da samun warkewar ciwo?In ji Dr Ahmad Inuwa na Garko clinic Danladi Nasidi housing estate Kano ya ce, ‘’Hankali shi ne mutum .Idan mutum ba ya cikin hayacinsa ba abun da ba zai iya yi ba.A kiwon lafiya magungunan nan da aka mayar na maye ko zuga mutane suna da amfani sosai idan aka bi kaidar su; wasu na ciwon jiki ne wasu kuma maganin mura wasu na sa barci wasu kuma na hauka ne ma. Idan mutum yana amfani da su ba a bisa kaida ba sai ya zamanto jikin sa ya saba har ya zamanto kullum kwakwalwar sa na bukatar sai ya sha.Magungunan sun kasu kashi daban daban da akwai wayanda ake kira opiods irin su methadone ana amfani da su ne dan maganin zafin ciwo Kaman mumunar rauni ko bayan an yi wa mutum theatre.Idan aka zarce da sha ya wuce kaida sai ya zamanto wa mutum farilla ya sha kuma zai yi koma menene dan ya samu.Shan su dayawa kuma yana iya kawo yankewar num fashi ko kuma mutuwa farad daya.”Likita ya yi mana bayani.
“Depressants kuma irin su diazepam,lorazepam da dai sauransu ana bada su a asibiti ne domin kwantar wa mutum da hankali da samo mishi sauki idan yana fama da fargaba ko kasa barci.Idan ya zama jiki kuma sai mutum ya sha kullum ya na sa yawan barci,rashin kuzari rudewa ,tabin hankali .Hadarin neman a daina sha ba da zuwa asibiti ba idan ya zama jiki kuma shi ne zai iya kawo lahani saboda haka idan an ga ne dan kwaya irin wannan magungunar ya ke sha a kai shi asibiti dan likita ya kulla da yanda za a raba mai sha da wannan halin.”
Abu Sufyan tsohon dan kwaya ne mai kokarin ya daina saboda haka sai naga ya kamata muji daga bakin sa me ke sa su shan maganin asibiti ba da dalili ko izinin likita ba me suke ji idan su kayi shaye shayen? ya wahalar daina sha  da kuma farashin magungunan.
Ya bayyana mana cewa,“Yawancin mutane wani damuwa ko baccin rai ke sa su su fara shaye shaye ko son samun wani Karin karfin jiki ko karfin guiwa idan za su je wani wuri ko za su yi wani muhimmin abu ama daga baya sai ya zamanto wa mutum jiki kuma ko nawa ne zai sa kudi ya saya.Magungunan basu da tsada irin su lara,d5,diyaga,assage,fashion duk daga naira 10 ne zuwa naira 30.Masu tsada irin su babban tramol ne wanda ake sayar wa N200.magungunan mura kuma daga N150 ne ama original daga N500 su ke.Gaskiya daina sha na da wuya domin matsalolin rayuwa dayawa.kwayan diyaga guda daya da ake sayarwa N20 sai ya warware maka duk wani damuwa da kake ciki.”Abu Sufyan.
Samari,yan mata da matan aure sun fi zake wa a wurin shan maganin mura dan maye ,idan aka je wasu wuraren shakatawa wayanda yan mata da samari ke zagayawa a dare guda sai a samu kwalban magani 100 a lokaci guda.Budurwa daya ana iya samun kwalba 5 a jakanta.Wasu matan auren kuma haka su ma suke tara kwalaben magungunan nan su yi ta sha sun mayar da shi Kaman sobo.
Ina iyayen da ke ba yaransu kudi su je su sha shisha?to su ma su kula domin shisha grade B magunguna ake sawa aciki kar yaran ku su tashi daga grade A wanda kanshi suke zuka ko kuma su koma grade C wanda wiwi ake sawa a ciki.
Wasu na fakewa da cewa shan magani ba haramun bane tunda ba giya bane.wannan babban kuskure ne domin babbu addinin da zai yarda da mutum ya sa kansa a hali na maye ko bata rayuwarsa.Magani kyan sa mutum ya sha iyyaka kai’dan da masana su ka bada ba wai ka ji labarin wani kwaya na sa barci ka kama sha ba kulla ba.
Maganin wannan illa kuma na farko shi ne fadakarwa,idan jamaa duk aka farga za a iya sa ido domin samun maganin wanan musiba da buwayi al-umma.a rika kulawa da yara da irin mutanen da suke muammala da.Idan an ga chanjin yanayi ko da mutum ya karyata shan kwaya haka siddan a je asibiti a bincika.

Sanjay da bishiyar Goba


SANJAY DA BISHIYAN GOBA

Ma su kallon fim din india dai sun san mutan India da nuna soyayya,bajinta da kuma rashin yafiya idan aka yi musu laifi tun balanta idan laifin ya taba mutuncinsu.

A  shekarar da ta gabata ne kafofin yada labarai na India suka kawo labarin wani dan tahaliki mai suna Sanjay.

Sanjay dai   an bada labarin cewa shekarunsa 25 ne kuma dan kauyen Ramgaon,Vinasi ne ama yana aiki a babban birnin Mumbai.Ya yi aure da wata mai suna Tara kimanin shekara daya.A  ranar 9 ga watan Maris Sanjay ya dawo gida daga aiki kafin lokacin tashin sa yayi,sai ya tarar da matarsa a cikin halin da bai kamata ba da wani makwabcinsu anan cikin gidan Sanjay din.Rigima ya kaure har sai da aka koma kauye yin sharia.

Zuwa kauye sai ya zamanto bai kawo karshen rigimar ba domin ita Tara bata ba wa mijinta hakurin cin amanarsa da ta yi ba.Malam Sanjay da ya ga ta ki ba shi hakuri bayan yan uwansu sun shiga maganar domin warwareta ya sa Sanjay ya zuciya ya hau kan wata bishiyar goba da ke nan kusa da gidan iyayen sa.  

A cikin watan disamba na shekarar 2012 dai Sanjay watan sa tara  a kan wannan bishiyar domin Tara dai bata ba shi hakuri ba kuma ta hada kayanta ta koma birni wato Mumbai bata daka ta tashi ba.

Kanwar Sanjay mai suna Nisha ta tabbatar wa jaridar Asian Age na India da aukuwar wannan abu;ta kuma kara bayani cewa yayan nata a kan bishiyar yake yin komai, anan yake cin abinci, anan yake barci ,anan kuma yake yin bawali da bahaya.Da farkon zaman sa kan bishiyar ya’yan itacen kawai yake ci ama daga baya mahaifiyarsu na kai mishi abinci.

A nan abun tambaya shi ne;zuciyar me ya sa shi zaman kan bishiyar?Idan ta ba shi hakuri me zai kara mishi?

Tambaya na biyu kuma shi ne; yana yaji ne akan yana son matar tasa ta ba shi hakuri su koma zaman auren su haka?