Saturday 5 September 2015

Bunkasa harkokin yan kasuwa


A ranar 12 ga watan Janairu na shekara 2013 ne mata suka yi wani dan karamin gangami a cikin garin Kaduna. Taron gashi ba na karatu,siyasa,biki,mutuwa ko suna ba. Ama ya sa wayanda suka halarta kwadayin samun daman zuwa wani.
Kamfanonin Aim Multimedia Concepts da Greenberry tare da hadin gwiwar wasu mata da suke muamala da su ne suka hada hannu.
Gangamin dai anyi shi ne a wani cibiya da a ka kafa domin zuwa motsa jiki.Akwai wuraren motsa jiki da dama a garin Kaduna.Ama kwadayin wannan hadin gwiwar kungiyoyin mata shi ne su samu su motsa jiki a wurin da babu  maza ko da masu koyar da motsa jikin ne.
Lafiya dai uwar jiki ce,ama matan mu na arewacin Najeriya suna sakaci da kula da jikin su ta fannin motsa shi.Daga bude  wannan cibiya mata su ka yi cincirindo   dan su koyi rawan zumba wanda yake sa mutum ya rame a cikin gajeren lokaci.
Kudi yana da nasaba da lafiya a zamanin nan.A bisa wannan dalilin ne a ka gayaci mata su zo su ga yanda ake rawan Zumba dinnan.Sannan a ka bama mata masu saye da sayarwa a gida ,shago ko kasuwa da kuma wayanda kasuwar ranar kadai za su ci daman su zo su baje kolinsu na yini guda.
Mata da dama suna sanaa ko saye da sayarwa ama rashin kasuwa ko kuma bashi na karya jarinsu.Wannan dama da aka samu tamkar kasuwa ce aka bude na yini guda,gashi ba maza,ga wadatacen fili ga haja .Masu sayar da abinci ma an same su kala daban daban.
A fanin gyaran jiki da bunkasa kasuwancin ana samu karfin gwiwa daga FashionHouse Kaduna,wanda yake a Wurno road kusa da ofishin NEMA. Katafaren gida ne da ake yi wa mata gyaran gashi,jiki da kuma dinki.A shekaran daya wuce sun koya wa mata hanyoyin motsa jiki dan samun lafiya inda suka kawo Fatima Adamu daga Philadelphia na kasar Amurka dan koyar da kwas na sati uku a cibiyar ta su.Ban da haka sun gudanar da baje koli har biyu dan masu kamfanoni da sana’a su talata kayan su.
Ga wayanda basu samu halartar wayannnan taron na baya ba;ranar 16 ga watan maris 2013 za a samu dama dan masu kasuwanci a gida ko a waje su talata kayan su.Ga mazauna Kaduna da kewaye  sunan Wusasa Business school da UWIDI ba bakin sunaye bane wurin koyar da harkar kasuwanci,tallafi da kuma kare mutuncin mata da kimarsu ta fanin dogaro da kai.
A kan wannan manufa ne suke shirin yin Taro da suka   sa ma suna;’ Baje kolin kanannan yan kasuwa’.A bayanin kakakin hadin  gwiwar AIM,WBS da UWIDI Kabiru Abdulkadir yin wannan taron ya zama dole ne domin magance wasu matsaloli da ke fuskantar kananan yan` Q kasuwa da kuma masu sanaar hannu.
A bayaninsa ya ce;”Mutane dayawa suna kasuwanci ama sai ka ga basu san hanyoyin zamani da za su yi amfani da  ba domin bunkasa neman kudinsu. Wannan karamin baje koli ba irin wanda a ke yi na gwamnati bane;baje kolinmu na da riba 5. Na daya ba bashi kowa da kudinsa zai koma gida .Na biyu kasuwa cikin bainar jamaa ba zancen ba a san kana sai da kaya  ko sana’aba.Na uku halartar bita kyauta a kan bunkasa kasuwanci da zaban sana’a.Na hudu talla a cikin mujalar kasuwanci na AIM da za a kaddamar a ranar wanda ko bayan ranar mutane sun san inda za su neme ku  da kayan ka.Na biyar kudin baje koli mai rahusa wanda ko dan makaranta zai iya kama shago na yini guda.
Baje kolin za ayi shi a ranar asabar 16-3-13 a Womens multipurpose center,Bank road Kaduna.Daga karfe sha biyun rana zuwa karfe shida na yamma.Ma su neman Karin bayani za su iya samun Mal Kabiru a kan lamba 07038000480.Ma su karatun shafin nan da ke da tambayoyi akan harkokin mata su nemi ma’aikatan UWIDI a wajen dan samun shawara kyauta.

No comments:

Post a Comment