Wednesday 23 May 2012

KE WACCE CE. (WHO ARE YOU?)


“Ke wacce ce?Ke din banza! kina mace ki ce za ki gaya min abun da zan yi, ko ya kamata in yi? Kin fara hauka ne?Uban ki ma bai isa ya gaya min abun da zan yi ba balantana ke,sha sha sha, sakarya kawai, daba.”

Wannan kadan na dauko daga cikin shariar wani aure da aka yi a gaba na.Mata ce ta ba wa mijin ta shawara akan yan da zai rika tafiyar da harkokin sa na kasuwan ci tunda kowa ya san yau da wuya komai yayi tsamari a kasar.Da mijin ya tashi zagi ,mahaifinta ma sai da aka zage shi bai ji ba bai gani ba. Wannan shi ne Nasara ke kira abusive relationship wato dangantaka da ake yi wa cin mutunci ko cin zarafi.Me ke kawo cin zarafi tsakanin maaurata?Ina neman Karin bayani da haske dan mu samu mu fahimci wannan mumunar dabiar ta wasu maza da mata a gidajen su domin kokarin magance shi.

4 comments:

  1. A ra'ayina, ba wani abu bane ke kawo cin zarafi da mummmunar dabi'a tsakanin ma'aurata kamar irin wannan sai wadannan dalilai
    1. rashin sanin mahimmancin aure da danne hakkin mata ko miji
    2. neman a wulakanta mata domin ta zama bata ganin kanta da daraja sai yadda a ka yi da ita
    3. miji na ganin shine ne a sama kuma mata su kaskantattu a cikin halitta
    4. shi mai yin wannan ba ya ganin mutuncin da darajar kansa saboda haka bai san mutuncin ko darajar wani ba

    ReplyDelete
  2. I see the husband as an uneducated guy who did not receive proper upbringing. He might as well have been brought up by a 'goat'.

    ReplyDelete
  3. Ko da namiji ya taso da tarbiyya mai kyua, zaiiya chanjawan sabo da gadarar shune a sama da matar. Sannan kuma wani lokacin ganin Allah ya hore masa abun hannu sai ya dauki girman kai ya daura a kansa, ba wanda ya ia ya bashi shawara ganin cewar yana da abin hannun sa. A wasu lokutan kuma karancin Ilimin Addini in musulmai ne shike sa mazaje ke irin wannan dabiar. Wasu mazan kuma suna da ilimin amma kawai rashin sanin yakamata. Amma inaga na suna zama suyi reflecting a kansu, na in akayi wa yarsu ko qanwarsu ya zasu ji, to wataqila baza suyi wani abun ba.

    ReplyDelete