Friday 18 January 2013

KISHI KUMALON MATA



                                          
Masu iya Magana suna fadin cewa duk macen da ba ta da kishi to bata cika mace ba ta rako mata duniya ne.Wai mata kadai ke da kishi?.Mene ne kishi kuma me nene mahimmancin sa a rayuwar dan adam.Kishi dai shi ne mutum ya ji rashin dadi da zaman wani ko samun sa ko zamantakewar sa ko ta hanyar soyaya,ko abun duniya ko ilimi ,ko kasuwa ko girma a wuri.Kishi kuma zai iya zama cewa mutum ya razana da shigar wani rayuwarsa ko rayuwar  wani ko wata da suke da kusanci ko kuma hanyar samu. Wata ya’ya ta tana cewa ko almajiran da suke layi karban sadaqa a kan titi ana samun kishi da hassada a tsakaninsu.Kishi ya dauko asali tun halartar dan adam, ba sabon abu bane ba kuma abu bane da za a ce yana da karshe ba sai dai a samu saukinsa da kuma halaya da ke zama daban  daban.
A kan kishi mutane dayawa sun halaka a duniya kuma dayawa za su halaka a lahira.Me nene halarcin kishi a addini?Halal ne ko haram,malamai sun yi bayani akan kishin da ya halarta shi ne kishi a wajen yawan ibada da kusanci da ubangiji.
A duk sanda mutum ya fita daga gida ya zaga unguwa,ko kuma ya saurari kafofin sadarwa idan yau ba ka ji ba, gobe ka ji wani mumunan aikin da kishi ya kawo.A ranar 6-9-12 labarun yahoo na yanar gizo ya kawo labarin wani dan wasan kwalon kafa a kasar ingila da ya kashe budurwarsa yar shekara goma sha biyar  domin kishi.A cikin watan da ya wuce ne na ga wata mata da budurwar mijinta ta bi ta har gida ta kama ta da kokawa, ta kwasa da gudu  budurwar ta hangi ruwan zafi ana dafawa a gefe ta dauka ta watsa a bayan matar nan,wa yanda suka san labarin sun tabbatar da cewa budurwar har a yau basu rabu da mutumin ba, mata ita ko jinya bai kare ba.
Maza na lahanta ko kashe abokan gaban su a wurin neman dukiya;a kasuwanci ,sarauta ,siyasa,aikin office ,soyayya da sauransu. Mata ma  na nasu kokarin a wurin kishi tun balanta a wurin soyyaya ko aure .Wata babbar mace da muka yi hira da ita a Abuja tayi mana tadin wata mata da budurwar mijinta ta biya yan fashi dasu tare matar a hanya su kashe ta domin mijin ya ki aurenta kuma a tunanin budurwar lefin matar ta gida ne.Maman Hauwa ta yi mana bayani cewa,”wata mata ce a nan garin Abuja mijin ta na da kudi da mulki sai ya zamanto cewa akwai budurwar da suka dade tare ama bai aure ta ba,da matan da budurwar duk sun yi iyaka kokarinsu a wajen malamai,bokaye,pastoci da dai sauran masu ba da taimako.Idan ita budurwar ta nemi samun kan mutumin sai matar ita ma ta zaga ta rusa.To a haka ne budurwar abun ya ishe ta ta ga gara ta aika ta lahira ta huta gabadaya.
A zahiri babu wanda zai so a ce wani ya fi shi a wani abu,ko kuma an fi son wani a kan sa,ko abun da mallakar ka kai kadai ne yau an wayi gari sai dai ku yi taraya da wani a kai.
Asalin wannan rubutu ya taso ne da na samu labarin kishiyar kanwata Allah ya yi mata rasuwa. Ita kanta kanwar nan tawa Binta na yi shekaru ban gan ta ba dan nisan garin da ta ke aure ama tare muka taso a ka yi mana aure.  San da ta aure  Isa  bai dade da fara aiki ba kuma ba shi da komai da sunan abun duniya,ba ta kaunarsa ko kadan ama ta bi umarnin iyaye ta aure shi kuma ta zauna.Isa ya taba aure har da da daya sai suka rabu da matarsa ,ganin ba zai zauna haka ba ya sa a nemo mishi wata ya aura.Aka hada shi da Binta suka yi aure.Abun da ya daure wa mutane kai shi ne,ita Binta tana da zafin kishi da gasa,ba ta son kowa ya fi ta da komai. Abun mamaki sai ya zamanto ita da kanta ta nemi matar mijin ta na da suke zumunci.Isa  ya nuna ba ya so ama bata daina ba har wata rana matar mijin ma ta zo gidanta suna hira Isa ya dawo gida kwatsam. Ita Binta ce ta boye matar nan ta shi a dakin ta a cikin wardrobe. Shekara da shekaru suka wuce Allah ya albarkaci zamansu da yaya  da rufin asiri.A wannan lokacin ne Isa ya kawo maganar yin aure.Abu na dangi ni da nake gefe labari na ji ama sai da na taya ta kishi tun balanta na ji an ce amarya ita                                                                                          za a kai abuja Binta ko an ajiye ta a gefe wai yaya sun yi mata yawa.yau sai aka wayi gari wai amaryar nan Allah ya dau kayan sa,Sai na ji kunya.Daukan dimin na mene ne,yau da Binta ce ta rasu ai  wannan baiwar Allah ita za ta rike mana yaya.Allah dai ya shirye mu ya ganar da mu.
Kowa ya san kishi ya san abun da yake iya jawo wa,abun da mutane dayawa ke   tambaya shi ne ta yaya za a rage kishi ko kuma a ci moriyar kishin nan? Ga mabiya addinin Islama da akwai adduoi da ake iya karantawa domin rage zafin kishi. Da akwai wasu hanyoyi da zamu iya amfani da su domin gane idan muna da kishi da ya wuce hankali da kuma yanda za mu rage zafin kishin. Ku biyo mu kashi na biyu na wannan rahoton wata mai zuwa domin karanta wayan nan hanyoyin.
Saadatu Hamma
 Kaduna
9-9-12

No comments:

Post a Comment